Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tambayoyi da amsarsu tare da
Mallam Ibrahim Zakzaky na talatin da hudu


Sayyed Zakzaky2

TAMBAYA: Ni ina zaune ne a inda akasarin mutane ba sa azumi sai sun ga wata da idonsu. Saboda haka sai nake bin su muna yi tare. Amma in na je inda ake yarda da ganin adilai, to su ma sai na bi su. To yaya matsayin Azumin nawa? Daga Ibrahim Yusha'u Unguwar Naladi Dabai.

SHAIKH ZAKZAKY: To ka'idar addini za ka bi. Ba za ka yi la'akari da ya ake yi a wancan garin ka bi na 'yan garin ba. In kuma ka je na wancan 'yan garin su ma ka bi nasu. Ka'idar addini shi ne ganin adilai, ba sai mutum ya gani da idanunsa ba. Saboda haka in ka bi shari'a, to, shi ne daidai, in kuma ka bi son ran wasu, to abin da hukunci ya hau kanka la'alla kaffara ne.

TAMBAYA: Kamar yadda aka ce idan mutum zai yanka dabbar da take cin najasa, sai ya killace ta zuwa wasu 'yan kwanaki, to menene hukuncin kazar da mahauta suka yanka?

SHAIKH ZAKZAKY: To idan ba a yi mata istibra'i ba, abin da ya fi alheri shi ne a guji ci din. In har ana tsammanin ta ci najasa din. Amma in ba ka sani ba shi kenan sai ka kaddara lafiya lau ne. Ba kawai daga ka ga nama sai ka kama tambaya, to yaya yake? Sai ka kaddara yana da kayau. Amma in kai ne, abin da aka ce za ka yi kenan.

TAMBAYA: Ko ya halasta musulmi ya nemi auren kirista alhali ba shi da tabbacin in ya aure ta za ta musulunta? Daga Garzali D Gumel

SHAIKH ZAKZAKY: To, a inda aka yi maganar auren wadda take ba musulma ba, wato 'yar ahlul kitabi, lallai ba a ce da sharadin za ta musulunta ne ba dama. Za ta zauna a addininta ne, amma za ta bi ka'idojin zaman aure irin na Musulunci.

A bisa fatawoyin Imam Khomaini, yana ganin wannan sai dai a bar shi a aure 'muwakkati,' amma a aure 'da'imi,' abin da ya fi 'ihtiyadi shi ne a guje shi.

TAMBAYA: Menene hukuncin auren kwarkwara da Sarakuna suke yi, kasantuwar yanzu babu bayi? Daga Gazali D Gumel

SHAIKH ZAKZAKY: To lallai ban san wani abu sunansa auren kwarkwara ba. Abin da aka sani dai shi ne akwai aure, akwai mallakar dama, wanda shi mallakar daman yanzu ya riga ya kau babu shi, tun da ba mutane a kasuwa wanda ake sayar da su ba tare da wani ka'ida ba.

TAMBAYA: Ko ya halasta miji ya bai wa matarsa guru ko laya ko maganin Bature ko na gargajiya, wanda zai hana matar daukar ciki lokacin da take shayarwa don gudun ka da cikin nata ya shafi abin da take shayarwa? Daga Muhammad Khamis Kasuwar Murtala, Kana.

SHAIKH ZAKZAKY: To, in dai tsayar da ciki ne, abu daya da za mu iya kwatanta shi da shi, shi ne 'azalu,' wanda aka ruwaito ana iya yi. Shi ne fid da saduwar maniyyi ya zuwa farjin mace. Kuma daga nan ana iya kwatanta shi da wadansu dibarori da ake yi, ko sa kwaroron roba, ko wani abin da ya yi kama da haka nan, ko shan wadansu magunguna wanda duk ba za a iya harantawa ba matukar ba zai yi illa ga matar ba. Amma lazim ka tabbatar da cewa; abin da za ka bayar din, wani abu ne da ya inganta yana iya hanawa. Amma ban san wani guru ko laya wanda aka ruwaito yana hana daukar ciki ba. Sai dai ya zama kawai dibarori wanda a da can suna amfani da 'azalu' kuma an ruwaito shi ya halasta, kuma yanzu mutane na amfani da kwaroron roba, suna kuma shan magunguna. Amma wala'alla in guru ne, ka ga ba ka san menene ba, wala'alla kila ma surkulle ne, ko tsafi. Wallahu a'alam. Amma dai in dai abin da za a yi amfani da shi ya halatta a shari'a, to wannan babu laifi da shi. Sai dai barin yin wannan ma shi ne ya fi alhairi gaba daya.

TAMABAYA: Menene halascin cin fara da wasu ke ba da fatawar halascinta? Daga Muhammad Khamisu Kasuwar Murtala, Kano

SHAIKH ZAKZAKY: To, lallai ba wani laifi. Tana daga cikin abubuwan da ba su da jini mai gudana, kuma mutuwarsa shi ne yankansa. In mutum ya duba zai ga cewa tafiyarsu daya da wadansu jimlar wadansu abubuwa irin wadanda suke ba ana yanka su bane. In yana so ya ji sahihancin ne, eh haka ne ana ci.

TAMBAYA: Menene ingancin hadisin da aka ce wani mutum ya mutu ana bin sa bashi, Annabi (S) ya ki ya yi masa salla har sai da aka biya bashin? Daga Muhammad Khamisu Kasuwar Murtala, Kano

SHAIKH ZAKZAKY: To ni ban san bayanin wannan hadisin ba. Amma dai abin da na sani shi ne sai an gama ma batun salla an kai mutum, wanda yake wajibi ne cikin wajibobin addini, sannan ake batun rabon dukiya na gado, sannan ake batun wasiyya da kuma bashi. Amma wajibin farko shi ne a yi masa salla, sai dai akan tambayi wasiyya wanda ta shafi salla din. Alal misali, kamar ya bar wasiyyar cewa wani ya yi masa salla, to sai a kaddamar da wannan wanda ya ce ya yi masa din. Amma in ba haka ba, lokacin maganar bashi bai taso ba har sai an zo rabon gado, wanda kuma ba shi ake farawa da shi ba. Da salla ne da bizne mutum, wadanda suke wajiban farko, da su ake farawa.

TAMBAYA: Mutum ne yake zuwa aiki a makare, wasu lokuta ma ba ya zuwa saboda gwamnati ba ta biyansu hakkokinsu. Shin albashinsa da yake karba ya halasta a gare shi? Daga A.A Bature, Ministry of Petroleom Resouces, Abuja.

SHAIKH ZAKZAKY: To, aiki dai yana da ka'ida wadanda yake lazim akan rubuta wadannan dokokin, kuma a kansu ne ka karbi aiki din, to zai kuma zama wajibinka ka cika wadannan ka'idojin, in ba su cika maka ba sai ka bi hakkinka, amma ba ka da iko kai ka tauye nasu hakkin, sannan ka ce ya biya wancan. To kai kanka ka ce akwai albashnka. Ala'ayyi halin makoma a nan shi ne ka'idar aikin da ka sa wa hannu har ka yi rantsuwa a kai.

TAMBAYA: Mutum ne ya yi amarya sai ya yi mata saye-saye da kuma ba ta jari. Shin dole ne sai ya yi wa uwargida makamantansu alhali ya yi mata nata lokacin da ya aure ta? Daga A.A Bature, Ministry of Petroleom Resouces, Abuja.

SHAIKH ZAKZAKY: To, dama dai ba shi daga cikin abin da aka lizimta masa, cewa in ya yi aure sai ya ba matarsa jari. Amma akwai da ma wadansu saye-saye daidai gwargwado wadanda aka san a lokacin zuwan amarya za a bukata, wanda yake ita uwargida kila tana da irin wadannan. Sai dai bisa kyautatawa, in amarya za ta zo ita ma uwargida ana gyara mata dakinta ita ma da wadansu abubuwa shigen irin na amarya din, ko da bai kai nata ba. Jari ba a san shi ba kam. Ba a san ana ba mace jari ba. Amma lallai in ya ce ya ba da jari, zai zama adalci ya ba ita ma uwargidan. Idan ya ce yana ba da jari ne shi tun da yake haka yake yi, to lalle uwargidan ma sai ya ba ta jarin.

TAMBAYA: Idan yaro ya rasu, nakan ji ana cewa Allah ya sa shi cikin kaffalar Annabi Ibrahim. Menene kaffalar, Aljanna ce ko kuwa? Daga Zakariyya Lawal, Madrasatul Fudiyya, Dabai jihar Katsina

SHAIKH ZAKZAKY: Wato tun da Annabi Ibrahim shi ne Babanmu a addinance, ana fata shi wannan jariri a sa shi ya zauna karkashin renon Babansa, Ibrahim. Wato Allah ya sa shi karkashin renon Annabi Ibrahim. Ana cewa haka nan.

TAMBAYA: Jin kunyar surukai ko dan fari ko mijin fari da mata ko maza ke yi, har ana cewa ba kyau fadar sunan suruki ko dan fari da makamantansu. Shin menene halasci ko haramcinsa a Musulunci? Daga A'ishatu Bashir Gadar Maiwa,Ningi jihar Bauci.

SHAIKH ZAKZAKY: To, wannan lalle babin haramci ko halasci bai ma taso ba, saboda wannan wadansu abubuwa ne na al'adun mutane, wadanda yake kuma al'ada in ba ta saba wa shari'a ba, babu laifi da ita. Ko wadanne irin mutane suna da al'adu. Shari'a ba ta yi magana dangane da wannan ba, amma ba yana nufin sun saba wa shari'a bane. Idan al'umma tana ganin wani abu abin kunya ne wani ya yi, to ana bukatar ya kiyaye, sai dai idan shari'a ta tilasta shi ya yi wannan abin, amma a al'adarsu abin kunya ne, to, ba zai koma wa al'ada din ba tunda shari'a ta ce masa ya yi dole. Ko shari'a ta ce ya bar abu dole, to idan al'ada ta dauka abin kunya ne barin wannan, to, dole sai ya bari din, shari'ar zai koma. To wannan kuwa wadansu abubuwa ne da ba a san su a shari'a ba. Saboda haka al'ada yadda ta sanya su, mutum in ya yi wannan babin al'ada, babu wani laifi da shi. Ko ba komai a ganin masu irin wannan al'adun, in mutum ba ya yi za a ga kamar ba shi da kunya ne.

TAMBAYA: Idan mutum ya karbi jinginar gona zai rinka ba da wasu kudi ne duk shekara ko kuwa? Saboda na ji an ce idan ba ya ba da wa, to kudin da ya jingini gonar suna raguwa ta yadda idan mai gonar ya tashi karbar gonar ba sai ya ba da wani abu ba. Shin yaya abin yake ne a Musulunci? Daga Abdullahi Aliyu Unguwar Tudun Wada Nasaru,Ningi jihar Bauci.

SHAIKH ZAKZAKY: Wannan babin jingina kenan, kuma magana ce mai tsawo. Abim da muka sani dangane da jingina shi ne, mutum yana ba da wata kaddara ce a matsayin garanti a ba shi bashi. To wanda ya karbi wannan kaddara din zai ajiye har sai ya biya shi bashin ya ba shi kayansa. Saboda haka idan mutum ya ba da jinginar gona, to, za a ajiye gonar ne ba za a noma ta ba, ba za a yi komai a cikinta ba har sai ya biya bashin, sai a mayar masa da gonarsa. Sauran bayanai a duba babin jingina.

TAMBAYA: Menene hukuncin dan uwan da ya bude gidan kallo na bidiyo kuma ana kallon kowane irin kaset? Daga Abdullahi Pure Water, Ningi jihar Bauci.

SHAIKH ZAKZAKY: To, in an kalli alhairi yana da lada, in an kalli sharri yana da zunubi. Saboda haka ya kiyaye cewa alhairi za a kalla ba sharri ba.

TAMBAYA: Mutum ne yake kasuwanci daga wani gari zuwa wani gari, ya kan karbi kaya a hannun wani, amma kayan bashi ne, to amma idan ya sayar sai ya je wajen wani daban ya sayo wasu kayan da kudin. Meye hukuncin wannan? Daga Nasiru Inuwa kofar tashar Bauci, Jos.

SHAIKH ZAKZAKY: To, idan da ma yana ba shi ya sayar ne a matsayin ma'aikacinsa, to in ya yi haka nan, to ko ya sami wani kudi, kudin da ya sayo sai ya kai wa wancan. Ya ce, "na sayar maka da kayanka kuma na sayi abu kaza, ga kudin, ga kuma ribar da aka ci." To, amma idan da ma ya karbi bashi ne a kan zai biya, to, ba lazim ne wai don ya sami kudin sai ya je ya biya shi ba, sun ajiye lokacin biya. Saboda haka kudin yana nan a hannunsa har sai lokacin ajali ya yi ya je ya biya shi. Saboda haka tasarrufinsa a wannan kudin, bai mayar da cewa hakkin shi wancan da ya ba shi bane.

TAMBAYA: Ina sayar da man fetur ne, kuma ina amfani da galan gida biyu, kowannensu lita hudu ne, amma daya ya fi girma kadan. Shin ya halasta na zabi karamin in yi awo da shi? Daga Lawan Ahmad bakin tasha Janbulo,Gwaram jihar Jigawa

SHAIKH ZAKZAKY: To, adalci dai wajibi ne a dukkan harkoki, ciniki ne ko wani abu mai kama da haka. Saboda haka kar ka zama cikin sifar wanda in shi zai sayar, sai ya tankware, in kuma shi zai sayo, sai ya cika. Mai yiwuwa kai in da za a zo a sayar maka, kila babban za ka dauko, ka saya da babba, in ka zo sayarwa ka sayar da karami. Ya kamata ya zama bai daya ne. Bai kamata ya zama shi abin da yake awo wani ya fi wani ba.

TAMBAYA: Sannan idan mutum ya sayi mai kuma na cika masa galan, to amma kafin na zuba masa, kadan daga cikin mai din yakan zuba a kasa, ko wajen zubawa a mota ko mashin, amma wanda aka sayarwa ba sa yin magana. Shin ko ina da laifi? Daga Lawan Ahmad bakin tasha Janbulo,Gwaram jihar Jigawa.

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, in dai da gangan ne ka zubar masa da man kana da laifi mana, ka yi barna kenan. Sai dai idan irin wanda ba akan rasa bane bisa adatan yakan dan zuba, to wannan ba laifi.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


XtGem Forum catalog